Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar ‘yan sandan ta kasa ta kama wani mutum da ake zargi lauyan bogi ne, daya dade yana wakiltar jama’a a kotu a jihar Zamfara.

Rundunar ta gabatar da Chukwuka Jude mai shekara 46 a wani taron manema labarai da mai Magana da yawun rundunar SP Mohamaed Shehu, ya jagoranta a shalkwatan yan Sanda dake birnin Gusau.

Kayayyakin da aka samu a wajan wanda ake zargin wadanda rundunar za ta gabatar a matsayin sheda sun hada da, katin shedar aiki na bogi da hatimi da kuma takardun rubuta wasika da ke dauke da sunan kamfaninsa na aikin lauya ; J.N Monyei & Co.
Chamber.

A jawabin kakkakin ‘yan Sandan, yace a ranar 18 ga watan da muke ciki, shugaban kungiyar lauyoyi na jihar Zamfara ya gabatar wa da ‘yan sanda kara cewa, an kama wani mutum a cikin Babbar Kotun Shari’a da ke Tudun Wada a Gusau, yana gabatar da kansa a matsayin lauya ga wani.

Nan da nan kuma masu bincike na ‘yan-sanda suka shiga aikinsu inda suka damke mutumin, wanda a yanzu yake hannu, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike.

Binciken farko-farko yan nuna cewa mutumin ya dade yana gabatar kansa a matsayin lauya a kotuna da dama na jihar, da suka hada da a kananan hukumomin Kauran Namoda da Birnin Magaji da Shinkafi da kuma Gusau, inda a karshe aka kama shi yana wakiltar wani da ya karbi kudi a wurinsa yana wakiltarsa a matsayin lauya.

Rundunar ta ce mutumin da ake zargi a kokarinsa na tsere wa kamu da shari’a, yayi tayin bai wa dan sandan kotu cin hancin naira dubu dari uku, wanda jami’in ya ki karba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *