Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya sha alwashin cewa dole ne Hanifa Abubakar, dalibar ‘yar shekara biyar da mamallakin makarantarta ya kashe ta samu adalci.

An sace Hanifa ne a watan Disamba, daga bisani Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar Noble Kids Nursery and Primary School, Kano, ya kashe ta.

Mutuwar ta ya janyo cece-kuce a fadin kasar nan, inda tuni aka fara wallafa #JusticeForHanifa a shafukan sada zumunta.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammad Garba ya fitar a madadin Gwamna Ganduje ya ce, za a yi wa Hanifa adalci.

Gwamnan ya bayyana wasu daga cikin matakan da aka dauka kan lamarin a matsayin rufe makarantar da aka yi wa yarinyar kisan gilla ba tare da bata lokaci ba, kwace lasisin makarantar da dai sauransu.

Ya ce gwamnati ta damu matuka yadda mutanen da aka damka wa kula da yara suka zama masu kisa.

Ganduje ya kara da cewa gwamnati ta tuntubi iyalan Hanifa inda ya kara da cewa dole ne a yi adalci domin ya zama izina ga wasu.

Gwamnan wanda ya yabawa jami’an tsaro a jihar, kan daukar matakin da suka kai ga cafke wadanda ake zargi da hannu a cikin lamarin, ya bayyana cewa yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike gwamnati za ta bibiyi lamarin har ta kai ga gaci.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *