Kungiyar kafa ta Kano Pillars tana garin Ilorin babban birnin jihar Kwara da nufin samun maki a karawarsu da kungiyar kwallo kafa ta Kwara United a wasan mako na bakwai a kakar wasa ta 2021/2022 Npfl. Fagenwasannni.com ta rahoto.
Babban Kocin kungiyar Ibrahim A. Musa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake magana ga ‘yan wasansa a lokacin da suke atisayen da suka yi a filin wasa na Ilorin a yammacin Laraba.
Koci Ibrahim ya bukace su da su daure kuma su kasance cikin shiri don duk wani kalubale da za su iya fuskantar a wasan.
Ya bukace su da su kiyaye da halin da suka nuna a wasan mako na shida da kungiyar Niger Tornadoes a ranar Lahadin da ta gabata a Kaduna inda suka doke su da ci 1-0 ta hannun Mark Daniel.
Ina da yakinin zaku samu kuma da yardar Allah zamu bar jihar Kwara da nasara, Koci Ibrahim yafada.
A nasa bangaren kyaftin din kungiyar Rabi’u Ali wanda aka sani da Pele ya yi Alkawari cewa za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun faranta ran gwamnati da al’ummar jihar Kano da daukacin magoya bayan kungiyar a yau a wasan da zasuyi.
Sai masu gida zata yi baje kolin ‘yan wasa ashirin da suka buga da Niger Tornadoes Fc a ranar Lahadin da ta gabata in ban da mai tsaron bayansu na dama Mustapha Jibrin saboda ciwon da ya samu a haduwar da yayi da Timothy Danladi.
Jami’in yada labarai na kungiyar Rilwanu Idris Malikawa ya ce Timothy Danladi zai fara fitowa a yau ne tun bayan komawarsa kungiyar daga Enyimba Int’l Fc.