Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Darakta Janar na hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa (NITDA), Mallam Kashif Inuwa Abdullahi, ya sha alwashin mayar da Hadejia cibiyar fasahar sadarwa a jihar Jigawa.

Darakta Janar yayi wannan alkawarin a jiya yayin bikin aza harsashin gina wata makarantar zamani a Hadejia, da Gwamna Jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar ya yi.

Hukumar ilimin bai daya a matakin farko ta kasa (UBEC) ce take gina makarantar, tare da hadin gwiwar humumar NITDA da kuma hukumar sadarwa ta kasa (NCC).

Kashif Inuwa ya bayyana cewa hukumar NITDA za ta sake gina wata cibiyar fasahar sadarwa a kusa da makarantar domin tallafa mata da samar mata da kayayyakin na’ura mai kwakwalwa.

Darakta Janar ya bayyana cewa Sakataren Zartarwa na hukumar UBEC, Farfesa Hameed Bobboyi, ya yi alkawarin kammala ginin makarantar kafin karewar wa’adin gwamnati mai ci, saboda Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya kaddamar da ita.

Mai Martaba Sarkin Hadejia, Dr. Adamu Abubakar Maje, ya halarci taron, yayin da gwamnan ya samu wakilcin Sanata Ibrahim Hassan Hadejia.

Bayan kammala taron, Sanata Ibrahim Hadejia ya kaddamar da shirin raba kekuna ga dalibai mata dake yankunan karkara domin zuwa makaranta. An yiwa shirin lakabin EDUKEKE.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *