Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban kungiyar murya Daya ( One Voice Tamburawa ) dake garin Tamburawa a yankin karamar hukumar Dawakin kudu..Jawad Ahmad a.k.a Maikyauta yace burin kungiyarsu ta one voice shine tallafawa duk alummar garin Tamburawa tare da hada kan alummar yakin dan samar da alumma ta gari da kowa zai alfahari da ita,

A wata tattaunawa da shugaban kungiyar Jawad yayin rabawa wasu marayu kayan makaranta da kungiyar ta dinka musu a fadar dagacin Tamburawa ranar lahadi, shugaban yace irin wannan aiki dayane daga cikin manufofin kungiyar daya zama wajibi akanta na tallafawa marasa karfi dan karfafa musu wajen neman ilimi dan samun kyakykyawar rayuwa,

Jawad ya kara da cewa wannan kadanne daga cikin ayyukan da kungiyar ta tsara a wannan shekara inda ya kara da cewa da sannu zasu cigaba da ayyuka da zasu zama abin jin dadi da alfahari ga kowa da kowa, inda ya bukaci masu hannu da shuni da sauran alumma da kada su rungume hannu suna jiran gwamnati dan yi musu aiki musamman irin wannan aikin samar da kayan makaranta da suke hana yara marayu da ya’yan marasa karfi zuwa makarantar duk da rashin tsadar su inji Mai kyauta kamar yadda ake masa kirari

A jawabinsa. wakilin Dagacin Tamburawa Sani Umar Wakili yabawa yan kungiyar yayi bisa jajircewar su na hada kan matasan garin batare da gajiyawa ba abin da wakilin dagacin yace abin a yabane kwarai,

Wakili wanda ya bayyana jin dadinsa da samar da tufafin makarantar ga wadannan marayu ya ja hankalin sauran alummar garin musanman masu hannu da shuni dasu kyaykwayi wannan kungiya wajen tallafawa marasa karfi a abubuwan da suka gagaresu, inda ya kara da cewa Masarautar Tamburawa na farin ciki da alfahari da kungiyar One voice,

Da yake bayyana jin dadinsa da yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta kansila mai wakiltar Tamburawa a majalisar karamar hukumar Dawakin kudu Usama Alkasim cewa yayi ayyukan da kungiyar keyi ya wuce yadda ake tsamnani kuma abin shaawane na irin tunanin matasan na tallafawa alummar yankin a wasu abubuwa da alummar ke bukata,

Usama wanda ya jaddada goyon bayansa da ayyukan kungiyar yace haka ya sanyashi tsunduma cikin kungiyar ba tare da bata lokaci ba

Shikuwa Dr Muazu Shuaibu Tamburawa malami a Jamiar kimiyya ta jihar Kano dake matsayin Uba ga kungiyar cewa yayi kungiyar One Voice ta zama wata fitila mai haska duhu ga alummar garin Tamburawa musamman na yadda a kullum take girmama masarautar garin tare da neman shawarwari dan bunkasa cigaban alummar yankin.
A koda yaushe

Kimamani marayu arba’in.ne kungiya One Voice Tamburawa ta dinkawa kayan makaranta da mayar da wasunsu makaranta

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *