Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Masanantar shirya fina finan Hausa ta Kannywood tace a shirye take ta hada kai da duk wanda ya shirya taimaka mata ta hanyar bun kasa hanyoyin samun kudaden shigarta da kuma kayayyakin aiki na zamani domin yin gogayya da takwarorinsu na kasashen duniya.

Shugaban kungiyar taurarin fina finan Hausa ta Kannywood Celebrities Forum TY Shaban ya bayyana hakan, lokacin da yake zantawa da manema labarai yayin wani taron tattaunawar fuska da fuska da kungiyar ta shirya tsakanin jaruman Masanantar da kuma Abdussalam Abdulkarim AA Zaura.

TY Shaban yace a halin Yanzu masanantar shirya fina finan Hausa na cikin wani mawuyacin hali da take bukatar jajirtacce mutum wanda zai tallafeta, ta hanyar kara horas da masu shirya fina finai da masu bada umarni da kuma su kansu masu fitowa a fina finan da ilimin sana’ar ta yadda zata cigaba da tafiya daidai da al’adu.

Ya Kara da cewa duniyar fina finai ta cigaba, sai dai a bangaran Kannywood akwai bukatar fito da sabbin hanyoyi da dabaru domin bunkasa sana’ar.

Lokacin da yake jawabi bayan kammala taron da kungiyar taurarin fina finan Hausar ta shirya harma ta karrama shi, Abdussalam Abdulkarim AA Zaura yace, zaiyi duk mai yuwa domin kyautata sana’ar tare da dorata a gwadabe na zamani da dubban al’umma zasu cigaba da amfana.

Har ilayau yace Masanantar shirya fina finan Hausa nada matukar muhimmanci a cikin al’umma, domin suna bada gudunmawa wajan cigaban al’umma ta fuskoki da ban da ban, adon haka yace akwai bukatar tallafawa bangaran yadda ya kamata.

Aminu Shareef Ahlan, yana daya daga cikin mashirya taron, yace sau da da yawa Yan Masanaantar na taimakon Yan siyasa sai dai daga bukata ta biya ake mantawa dasu tare da kin taimakon sana’ar tasu, yayi fattan AA Zaura zai taimaka musu kamar yadda yayi alkawari.

Yakubu Muhammad guda ne cikin masu bada Umarni a Kannywood yac bayyana cewa; Masanantar Kannywood na bukatar samar da hanyoyin samun kudin shiga ta hanyar gina manyan gidajan kallo na zamani wato Cinemas tare da kara horas da Yan Masanantar ilimin sana’ar shirya fina finai a zamanance.

Jaruman fina finan Hausa da dama ne suka halarci taron ganawar, wanda suka hadar da Alhaji Kabiru Maikaba, Ibrahim Mandawari, Yakubu Muhammad, Ladidi Fagge, Kamal S Alkali, Mansura Isah, Baballe Hayatu, Samira Ahmad, Aminu Shareef Ahlan, Tijjani Faraga, Daddy Hikima Able, Shamsu Daniya da dai sauran su.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *