Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Tsohon dan wasan gaban Liverpool,El Hadji Diouf, ya bayyana sunan kasar da zata lashe gasar cin kofin kasashen nahiyar Afrika ta bana AFCON a kasar Kamaru. Fagenwasanni.com ta rahoto.

El Hadji Diouf ya bayyana sunan kasar Senegal a matsayin kasar da zata lashe gasar ta bana wadda za’a fara barje gumi a ranar Lahadi 9 gawatan Janairu,inda kungiyoyi guda 24 zasu kara da juna.

Kasar Kamaru wadda itace zata zama me ma saukin baki zatayi iya bakin kokarin ta wajen ganin ta lashe gasar yayin da itama kasar Algeria zatayi na ta bakin kokarin domin ganin tare Kambun ta kamar yadda tayi shekaru uku da suka gabata a kasar Egypt.

Amma duk da haka Diouf tsohon dan wasan kasar ta Senegal ya yarda dacewa ‘yan wasan na Aliou Cisse’s sune kan gaba wajen wanda zasu lashe kofin a bana bayan sunyi rashin nasara a hannun kasar Algeria agasar wadda ta gabata a shekarar 2019.

“Kungiya ta ta farko da nake ganin zata lashe gasar AFCON ta bana itace Senegal wadda tayi rashin nasara a wasan karshe wancan lokacin a hannun kasar Algeria,Amma inada tabbacin yanzu zamuyi nasara,” Haka Diouf ya fada a shafin hukumar wasan kwallon kafa ta nahiyar Afrika CAF.”

“Kome zamuyi ba tare da mun lashe kofi ba rashin nasara ce.Nasan cewar akwai kungiyoyi kwararru lashe kofin bazai zo mana da sauki ba kamar yadda muke tunani,” inji tsohon dan wasan Liverpool da Senegal El Hadji Diouf.”

Senegal dai tana rukuni na Ba agasar kuma zata kara ne da kasashe irin su Malawi, Zimbabwe da kasar Guinea.

 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *