Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya bayyana rasuwar Dr Ahmad Muhammad Ibrahim, fitaccen cibiyar Darul Hadith da ke Kano, a matsayin babban rashi na jiga-jigan masu samar da zaman lafiya da kuma tarin ilimin Hadisi.
Mutuwar a cewar gwamnan ta yiwa jihar sosai. Ya kara da cewa, marigayi malamin ya kasance hazikin malami, mai zurfin hazaka da asali, a cikin karantarwarsa na fadin manzon Allah Muhammadu tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.
“Ya kasance mai karfafa zaman tare a cikin lumana, wanda tsarin koyarwarsa ya kasance da nufin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin dukkanin bangarori da ma sauran su. Wannan babban rashi ne da ke tattare da bakin ciki da rashin maye gurbinsa,” in ji gwamnan.
Gwamna Ganduje ya bukaci malaman addinin Musulunci da su yi kokari tare da yin koyi da kyawawan halaye na marigayi Sheikh. Yana mai jaddada cewa, “Ya kafa ginshikin yadda ake yin Da’awa kuma ya bi abin da yake wa’azi. Mutum mai daraja ta kowane hali.”
Da yake ci gaba da cewa, “A madadin gwamnati da al’ummar jihar Kano, ina mika ta’aziyyarmu ga iyalan Sheikh Dr Ahmad Muhammad Ibrahim, ba wai iyalansa ba, Kano ko Nijeriya baki daya, duk al’ummar duniya baki daya sun yi hasarar wani abu mai wuyar gaske. ”
Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa dukkan kurakurensa, ya kuma saka masa da alherinsa da Jannatul Fiddaus.