Shugaban kasan ya sanar da haka ne a yayin da ake zantawa da shi a kafar talabijin ta Channels , yana mai cewa Jama’a su rungumi harkar Noma da kiwo wanda itace hanyar da zata bulle.
Yayin tattaunawar, shugaban Buhari ya yi magana kan wasu matsalolin da suka dade suna ci wa kasar nan tuwo a kwarya da suka hada da tsaro, tattalin arziki, siyasa da sauransu.
Buhari ya yaba wa kokarin mulkinsa tun bayan kama mulkin shugabancin kasa a 2015, game da irin hubbasan sa a manyan fannonin da suka hada da tsaro, inganta tattalin arziki da kuma yaki da rashawa.
Shugaban kasan ya lura cewa abubuwa sun cigaba kuma mulkinsa na cigaba da inganta tattalin arziki duk da halin da kasar nan ke ciki.