Tawagar manyan ‘yan wasan Najeriya maza ta Super Eagles ta isa birnin Garoua na kasar Kamaru domin tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka na 2021, AFCON da za a fara ranar Lahadi a kasar da ke gabashin Afirka. Fagenwasanni.com ta rahoto.
Tawagar ta isa birnin Garoua ne da misalin karfe 11 na daren Laraba a yunkurin da suke na shirin lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka karo na 4.
‘Yan wasa 25 daga cikin 28 da aka gayyata sun isa Kamaru tare da ‘yan wasan baya biyu, Jamilu Collins da Tyrone Ebuehi da kuma dan wasan gaba, Odion Jude Ighalo har yanzu ba su hade da kungiyar ba.
Gabanin tafiyar tasu, ‘yan wasan sun bayyana kwarin gwiwar cewa za su yi wa kasar abinda zatai alfahari a gasar.
Najeriya ta lashe gasar cin kofin nahiyar a karo uku daban-daban a shekarun 1980, 1994 da 2013 kuma tana ganin ta sake yin galaba gun lashe a Kamaru.
A ranar Talatar mako mai zuwa ne Super Eagles za su fara wasa a gasar ta AFCON da kasar Masar a rukunin D.