Barcelona da Bayern Munich dukkansu suna zawarcin dan wasan tsakiyar Guinea da Liverpool Naby Keita – a cewar El Nacional. Fagenwasanni.com ta rahoto.
– Roma da Milan suma suna zawarcin dan wasan mai shekaru 26, amma ana tunanin Barcelona zata iya sa hannu dashi a wannan matakin.
Keita a bude yake don barin Anfield saboda samun karancin mintuna na yau da kullun, duk da sauran watanni 18 da ya rage masa a kwantiraginsa.
– Jaridar Daily Mail ta ruwaito cewa Arsenal ta sanar da wasu abokan hamayyarta na Turai cewa sun shirya karbar tayin Pierre-Emerick Aubameyang a cikin kasuwar nan rmta Janairu.
An daskarar da dan wasan gaba na kasar Gabon daga rukunin Gunners a karshen makon da ya gabata sakamakon keta ka’idojin kulob din kuma za a iya saida shi idan aka gabatar da tayin da ya dace.
– Brighton da Crystal Palace suna zawarcin dan wasan Arsenal Eddie Nketiah – in ji jaridar Sun.
Kungiyoyin biyu suna son siyan dan wasan mai shekaru 22 a lokacin bazara, wanda shine dama ta karshe ga Gunners din don samun kudi yayin da ya kusa kawo karshen kwantiraginsa.
– Bayer Leverkusen kuma tana sha’awar Nketiah, wanda a shirye yake don neman karin mintuna na yau da kullun.
– Axel Tuanzebe zai ga karshen aronsa a Aston Villa bayan Steven Gerrard ya kasa ba shi tabbacin lokacin wasansa, kamar yadda jaridar Birmingham ta ruwaito.
Dan wasan na Manchester United – wanda ya cancanci wakiltar DR Congo a babban mataki – an dawo da shi daga abokan hamayyarsa na gasar Premier, kuma ya nufi Napoli a matsayin aro.
– Liverpool ta ayyana tauraron Olympiacos Aguibou Camara a matsayin wanda take so ta siya – a cewar Calciomercato.
– Milan kuma tana sha’awar dan wasan tsakiyar Guinea mai shekara 20, wanda da farko ya koma Girka daga Lille a bazarar da ta wuce.
Camara ya buga wasanni 25 a duk gasa ga Olympiacos, inda ya zura kwallaye biyar kuma ya taimaka hudu.