Gwamnatin jihar Kano a karkashin ma’aikatar raya karkara da cigaban al’umma ta kaddamar da shirin samar da wutar lantarki a yankunan karkara da aka fi sani da ‘Stand Alone’ a karamar hukumar Gabasawa da ke jihar.
Shirin wanda tsarin ne mai amfani da hasken rana wanda kamfanin fasaha na Shenzhen Lemi da Lemi Renewable Electricity Limited ke gudanar da shi, an yi shi ne a kan kananan yankunan karkara akalla 100, kuma za a biya tsarin na wani lokaci.
Da yake jawabi yayin kaddamar da shirin, Kwamishinan Raya Karkara da cigaban al’umma, Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso, yace shirin zai kuma samar da ayyukan yi ga dimbin matasa a fadin jihar tare da bunkasa zamantakewa da tattalin arzikin mazauna karkara.
Ya kara da cewa domin cimma wannan buri gwamnatin jihar ta kulla yarjejeniya da kamfanin da zai samar da kayan aikin hasken rana.Ya kuma tabbatar da shirin gwamnatin jihar na samar da duk wasu abubuwan more rayuwa da ake bukata a fadin kananan hukumomin 44.
Kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Murtala Sule Garo, wanda ya samu wakilcin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kananan hukumomi, Alhaji Laminu Sani, ya yabawa yadda gwamnatin jihar ta yi hangen nesa wajen kawo ci gaba ga al’umma.
Sannan ya yi kira ga jama’a da su yi amfani da damar da aka basu domin ta fi karfin wutar lantarki da injinan janareta araha.
Hakimin Gabasawa, Magajin Garin Gaya, Alhaji Sani Dawaki Gabasawa, ya godewa gwamnati bisa zabar yankinsa domin cin gajiyar shirin, ya kuma bada tabbacin goyon baya da hadin kan dukkanin sarakunan gargajiya domin cimma wannan buri.