Wani masani kan harkokin kasuwanci da bunkssa cigaban dan adam Alhaji Bello Shugaba yace ya shiga harkokin bunkasa cigaban matasa a wasan kwallon kafa ne da tunanin sauya fasalin harkar kan gaskiya da rikon amana,
Express radio ta binciko irin yadda Bello Shugaba yasha fama da karo da rashin gaskiya da cin amana daga abokan harkar wasan da suka kulla amana amma aka samu tasgaro,
A tattaunawar wakilinmu salisu musa jegus da wani makusacin Bello Shugaba kuma shugaban kungiyar waliyya fc Baba Alhaji ya bayyana cewa Bello ya hadu da mutane marasa gaskiya da dama a cikin harkar wadanda ya bawa amana amma suka bashi kunya saboda rashin gaskiya,
Baba Alhaji ya kara da cewa Alhaji Bello wanda burinsa shine ya taimakawa matasa dake da basira wasan kwallon kafa su cimma burinsu ya shiga harkar bayan harkokinsa na kasuwanci da ayyuka inda yake fidda dukiyarsa dan a bunkasa cigaban matasan wajen horar dasu da sama musu makoma mai dorewa a fagen wasan amma shekaru da dama babu wani sakamako,
Baba Alhaji wanda yace duk da rashin samun sakamakon da cin amanar da wannan dan taliki ya gamu dasu bai karaya ba balle ya fita daga harkar sabanin yadda wasu kan karya harsu fita daga ita
Bello Shugaba ya jure irin wahalar dayasha har saida ya samun lasisin shedar zama dillalin yan wasa na hukumar kwallon kafa ta duniya wanda kawo iyanzu yake alfahari da ita sakamakon jajircewa
,
Kawo iyanzu Bello Shugaba na nan da burinsa na samarwa matasa masu basira daga ko ina dama kamar yadda a yanzu yake da kafa da idanu a kasashen Maldova ,Ukraine da Kasar Belarus kamar yadda Baba Alhaji ya bayyana mana,
Shugaban na waliyya ya cigaba da cewa gwagwarmayar Bello Shugaba ba kowane mutum ne zai jurewa halin daya tsinci kansa a ciki ba laakari da yadda yake bada gaskiyarsa da amanar sa ga mutanen da ya gasgatasu amma sai a samu akasi,
Akhaji yace kaunarsa da cigaban matasan ne ya sanyashi kin fita daga harkar duk da irin zagon kasa da cin dunduniya da aka sha yi masa daga abokan harka,
Baba Alhaji yace ya tuna lokacin da wata dama ta samu Bellon Shugaba yakai wani yaro wata babbar kungiya a kasa amma akabi dare akabi rana saida aka cire wannan yaron daga kungiyar saboda sabanin raayi duk da cewa a baya mutanen sun amfaneshi,
Wani hanin ga Allah ance baiwa ce, hakanne ya kawo haduwar Waliyya fc da Alhaji Bello Shugaba wanda kawo iyanzu aka cimma yarjejeniyar sauya suna kungiyar daga Waliyya baya kimanin shekaru 30 zuwa S,
S.B.S FC wato Shugaba Business Solution,
Da yake amsa tambaya kan sauya sunan Baba Alhaji cewa yayi hakan ya zama dole dan sharewa Alhaji Bello Shugaba hawayensa da bakin cikin da aka kunsa masa a baya, inda yace ” bamu da wani abu da zamuce masa, ko muyi masa sabanin wannan kuma mun kulla alkawri tsakanin mu da Allah”
Dagane da irin yadda ake tunanin makomar kungiyar Baba Alhaji cewa yayi ” makomar mai kyauce kwarai laakari da yadda shi Alhaji Bello ke da kishin cigaban matasa a harkar wasan” bazamu gajiya ba kamar yadda shima a kullum ke fadi tashi a harkar,