Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugabancin kungiyar masu gidan kallo na jihar kano sun sanar da barin karkashin kulawar hukumar tace fina finai ta jihar kano Censorship Board,

A wani taro da kungiyar ta shiryawa ya’ yanta a ranar litinin a gidan kallo na Lahai dake kan titin Abdullahi Bsyero, Shugaban kungiyar na jihar Kano Sharu Rabiu Ahlan yace sabuwar dokar hukumar bude ido da yawon shakatawa ta jihar ta ambaci gidajen kallon viewing centre karara a cikin kulawarta,wanda hakan ya nuna cewa gidajen kallon sun bar karkashin kulawar Censorship Board,

Sharu ya kara da cewa daga yanzu duk masu gidajen kallon zasu maida lamarinsu zuwa waccan hukuma, abin da yace hakan wata damace da zata kara inganta alamura da samun daidaito na gudanar da sanaar,

Dan gane da wani sako da hukumar tace fina finai ke aikawa masu gidajen kallo inda suke umartar su dasu biya wasu kudade. Sharu Rabiu cewa yayi su dakata har sai abin da kungiya ta umarce su,

Sharu wanda ya yaba da irin goyon baya da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ke bawa yan kungiyar yace ya zama wajibi kungiyar ta yabawa gwamnati tare da bin dokokin da gwamnati ke bijirowa dasu musamman wannan sabuwar doka data daukesu daga karkashin censorship,

Sama da masu gidajen kallo dubune daga sassa daban daban suka halarci taron,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *