Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da babban sarkin Gindiri a karamar hukumar Mangu ta jihar Filato, Mista Charles Mato Dakat a gidansa.

An tattaro cewa an yi garkuwa da basaraken gargajiya a ranar Lahadi tsakanin karfe daya na safe zuwa karfe biyu na safe.

A cewar jaridar The PUNCH, mazaunin unguwar, Helen Bulus, ta ce, “Lamarin ya faru ne tsakanin karfe daya na safe zuwa karfe biyu na safe. ‘Yan bindigar sun je fadar sa da yawa.

“Ya kasance a fadar shi kadai, saboda matar ta yi tafiya zuwa Jos, kuma yaran ba su kusa. Tsawon sa’o’i ne dai aka yi ta harbe-harbe da ‘yan bindigar a fadarsa, inda jama’ar unguwar suka rika gudu ta bangarori daban-daban.

“Don haka, da safiyar yau, da gari ya waye, mun je fada sai muka gano cewa ‘yan bindigar sun tafi da basaraken.”

Shima dan majalisar mai wakiltar Mangu ta kudu a majalisar dokokin jihar Filato Bala Fwangje ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar dan majalisar, an baza jami’an tsaro a cikin jama’a inda suke ta tseguntawa dazuzzuka domin neman sarkin gargajiyan da aka sace.

Ya ce, “Lamarin abin takaici ne.

 

“Na tabbatar da faruwar garkuwa da wasu daga cikin jami’an tsaro. Na kuma yi magana da babban mai mulki, Mishkaham Mwaghavul na ƙasar Mwaghavul wanda shi ma ya tabbatar mani da abin da ya faru. A yanzu haka jami’an tsaro na cikin daji suna kokarin kubutar da basaraken da aka sace.”

Jami’in yada labarai na rundunar soji ta Operation Safe Haven, Manjo Ishaku Takwa, da aka tuntube shi, ya ce an tattara sojojin na Operation SAFE HAVEN da ke Gyambus zuwa yankin kuma suna kan bin sawun masu garkuwa da mutane.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *