Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A yayinda harkokin tsaro ke kara tabarbarewa a nigeria gwamna abdullahi umar ganduje ya bayyana cewar tarin miyagu nau’i daban daban sun samu mafaka a dazukan kasar nan
yabayyana hakan ne a yayinda ya kaiwa shugaba kasa muhammad buhari ziyara a jiya.

Dr. ganduje yana shaida hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai,bayan yagana da shugaban kasar,yana me cewa kawar da dukkan mugaye daga dazukan shine kadai zai warware matsalolin da ake fama dasu su.

Gwamna ganduje yace ayanzu dazukan  sune manya matsalolin kasar nan saboda sun zama matattarar yan ta’adda da yan fashi da makami, makiyaya masu aikata muggan laifuka ,inda  ya sanar da manema labarai cewar yamika roko ga shugaban kasar da yasamar da wata cibiya zata ta kula da dazukan, ta yadda za’a share duk wasu bata gari daga cikinsu.

idan ba’a manta ba a farkon fara tababarewar tsaro gwamna ganduje yayi kokarin samar da kwamitin tsaro na hadin gwiywar jami’an tsaro inda suka gudanar da sintiri a dazukan falgore da wasu gurare dan tabbatar da tsaron jihar kano .

 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *