Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya musanta amincewa da wani bangare na jam’iyyar All Progressives Congress a Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar a ranar Asabar.
“Fadar shugaban kasa na son yin tir da furucin da daya daga cikin bangarorin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano ya yi a bainar jama’a, cewa sun samu amincewar shugaban kasa Muhammadu Buhari,” in ji sanarwar.
”Wannan ba gaskiya bane a fili. Wannan ba zai iya faruwa ba lokacin da al’amura ke jiran hukunci daga kotuna”.
‘’Don a fayyace wannan, Shugaba Buhari bai amince da wani bangare ba’’.inji solacebase
A cewar sanarwar, goyon bayan sa ga jam’iyyar All Progressives Congress a matsayin jam’iyya ce, hadin kai da karfi, ba na kowane bangare ba.