Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A karo na biyu cikin sa’o’i 24, ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin da ke jigilar matafiya a hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari a jihar Kaduna.

An yi imanin an kashe mutane shida a harin yayin da aka yi awon gaba da matafiya da dama

Lamarin ya faru ne a Unguwar Geda, da ke ‘yan mita daga Zankoro, wani wuri mai ban tsoro da ke kan hanyar, da misalin karfe 3 na rana, a ranar Alhamis.

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce kanensa na cikin wadanda aka sace.

Wani mazaunin Udawa, Mohammad Umaru, ya tabbatar da cewa an kashe kanensa ma.

“Yana da muni; sun kashe dan uwana; Mun karbi gawarsa kuma muna shirin binne shi,” inji shi.

Kamar yadda Aminiya ta ruwaito, ‘yan bindigar sun karya lagon motocin da jami’an tsaro da ’yan banga suka yi wa rakiya yayin samamen.

Babu wani bayani a hukumance daga gwamnatin jihar da kuma rundunar ‘yan sanda kamar yadda kiran da aka yi wa jami’in hulda da jama’a na rundunar, ASP Jalige Mohammed bai amsa ba.

A baya dai rundunar ‘yan sandan ta ce an ceto sama da fasinjoji 40 da aka yi garkuwa da su ranar Laraba.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *