Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Azuba fc  Ahmad Zubair Baba yace kafa kungiyar wata damace da zata bawa matasa yan wasan kwallon kafa dake da burin zama wani abu a wasan cimma burinsu

A tattaunawarsa da wakilinmu shugaban kungiyar yace laakari da yadda matasan jihar kano ke da buri da son wasan kwallon kafa, hakan ya karfafa masa gwiywa na ganin ya kafa kungiya da zata manewa matasa mudubi da hanya da zasuyi amfani da ita wajen cimma bukatunsu a fagen wasan kwallo kafa,

Dayake amsa tambaya kan kalubalen da ya fuskanta kafin kafuwar kungiyar  Zubair Baba .yace ” Gaskiya an fuskanci kalu bale musamman wajen samun yan wasa inda wasu kungiyoyi suke kin sakin yan wasan, yayin da wasu yan wasan kuma suke raina kungiyar” inda yace ” munsha fama da kulab kulab amma daga baya an sami daidaito bayanda shugaban hukumar wasan kwallon kafa ta jihar kano Sharu Rabiu Ahlan ya sanya baki ”

Dan gane da yadda kungiyar ta sami kanta cikin rukunin ajin matasa na kasa Zubair cewa yayi akwai abin mamaki bayan samun damar shiga rukuni na uku, inda hakan ya bamu damar shiga Preseason na yan ” Amateur ” inda muka buga da manyan kungiyoyi abin da ya bamu damar samun rukuni na 2 bayan da masu ruwa da tsaki a harkar kwallon kafa a jiha da kasa sukaga dacewar mu shiga rukunin bayan taka rawa da yan wasanmu sukayi abin daya bawa mahukutan wasan kwallon kafa karfin gwiywar bamu damar samun gurbi a rukuni na 2 a ajin matasa, inda muka halarci gasar 2020/2021 a Jigawa tare da taka mahimmiyar rawa a gasar,

Dangane da abin da kungiyar tasa a gaba shugaban na Azuba fc cewa yayi yanzu haka kungiyarsa ta fara tura yan wasan zuwa waje da suka hadar da Ukraine da Dubai kuma yan wasan na kokari abin daya basu damar samun kungiyoyi da suke taka leda kuma abin da muke fata kenan inji Inji Ahmad Zubair Baba

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *