Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Tsohon darakta a kamfanin samar da man fetur na kasa NNPC Mslam Inuwa Ibrahim Waya yace bashi da wani buri da ya wuce ganin ya samar da kyakyawar makomar Ilimin ya’yan Jihar Kano musamman daga tushe,

Wakilinmu Salisu Musa Jegus ya Hakaito Malam Inuwa Waya lokacin bikin karramawa da kungiyar yan jaridu ta kasa masu rahoto Correspondent Chapel sukayi masa a Hotal din Tahir,

A bayaninsu na dalilan daya sanyasu daukar matakin karramashi shugaban kungiyar yar ta Correspondant Ibrahim Haruna  yace Aniyar Malam Inuwa Ibrahim Waya ta dawo da martaba da darajar Ilimi da farfado dashi batare da shamaki ba shine yaja hankalinsu tare da  samar da kayan koyo da koyarwa, kudade da wasu abubuwa da koyarwar ke bukata na daga cikin abubuwan da Malam Inuwa ke samarwa dan tallafawa yun kurin gwamnatin kano na samar da Ilimi kyauta,

Wani abu daya sake jan hankalin yan jaridar shine yadda kullum bakin Malam Inuwa Waya ke Magana kan Ilimi, shin ko meyasa Malam Inuwa ke batun Ilimi sabanin sauran abubuwa ?

A amsar da yake bayarwa Malam Inuwa Waya cewa yayi ” Na fifita maganar Ilimi fiye da komai, saboda shine ginshikin rayuwa” kuma dukkannin wani cigaba da kowace daukaka a doron Ilimi ya damfara, saboda haka bani da wani burin illa na taimaki alummata su sami Ingantaccen Ilimi inji Malam Inuwa Yakasai,

” zan kashe komai nawa, zan bada kowace irin gudummawa dan ganin matasan jihar kano sun sami Ilimi” Inji Inuwa Waya

Dan gane da hsrkokin siyasa Waya cewa yayi na shiga siyasa da kyakykyawar niyya da burin aiki tukuru amma Samar da Ilimi shine abu na farko dana ke son ganin Kano tayi fice a cikinsa, saboda haka matukar na sami wannan dama zanyi aiki kan samar da Ilimi managarci ga alummar mu ” Ilimin na Addini dana Zamani”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *