Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

 

Wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki kasuwar Pinau da ke yankin Pinau a karamar hukumar Wase a jihar Filato, inda suka kashe mutane 11 tare da jikkata wasu da dama.

An ruwaito cewa ‘yan bindigar sun kai hari kasuwar ne da yammacin ranar Lahadi.

Majiyar Jaridar Dimokuradiyya, a ranar 8 ga watan Disamba, ta ruwaito yadda mazauna wasu kauyuka suka koka da kwararar ‘yan bindiga a wasu kauyukan karamar hukumar Wase.

Mazauna yankin sun kuma yi zargin cewa akwai masu ba da labari a cikin al’ummomin da ke aiki tare da ‘yan bindigar.

Shapi’i Sambo, shugaban matasa a Wase, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust harin na baya-bayan nan, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

Wani mazaunin yankin ya shaida wa wakilinmu cewa a cikin kwanaki 10 da suka gabata ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama a yankin tare da karbar miliyoyin naira a matsayin kudin fansa.

Ya ce, “Suna karbar kudin fansa a miliyoyi. Wani lokaci suna karbar Naira miliyan biyu, wani lokaci kuma Naira miliyan biyar. Kwanaki ukun da suka gabata sun karbi Naira miliyan 5 kafin su sako wani mutum da suka yi garkuwa da shi kwanakin baya.”

“Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ubah Gabriel, bai amsa kira da SMS ba a lokacin da wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakinsa kan lamarin” inji Daily Ttust.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *