Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

Shugaban FC Barcelona Joan Laporta ya gana da Babban Dillalin yan wasan kwallon kafa Mino Raiola a Italiya a yayin da ake rade-radin cewa kungiyar ta Spaniya ta shirya sayen Erling Haaland da Paul Pogba.

(Source: Fabrizio Romano)

#fagenwasanni

 

Everton, Leicester da Newcastle na son dan wasan baya Pontus Jansson, wanda kwantiraginsa zai kare a Brentford a bazara. (The Guardian)

#fagenwasanni

 

West Ham na zawarcin dan wasan baya Nathaniel Phillips, amma Liverpool na bukatar fam miliyan 10 domin ta bar shi. (Sun)

#fagenwasanni

 

Dan wasan Italiya Andrea Belotti zai iya barin Torino a matsayin kyauta a watan Yunin 2022. “Babu wata babbar damar tsawaita kwantiraginsa, amma za mu gani”, in ji shugaban Torino Urbano Cairo ga Sky Sport.

Torino tayi masa tayin sabon kwantiragi amma har yanzu babu wani abin da ya amince.

#fagenwasanni

 

Chelsea na shirin sabunta kwantiragin Thiago Silva. Sabuwar yarjejeniya har zuwa Yuni 2023 da za a kammala nan ba da jimawa ba. Majiyoyi na ganin tsawaita kwantiraginsa a matsayin ‘matsalar lokaci’

Thiago Silva yana so ya ci gaba da zama kamar yadda yake son rayuwa a Chelsea – hukumar kungiyar da Tuchel suna matukar farin ciki da shi … [Sky Sport]

#fagenwasanni

 

Sabunta tayin tsawaita kwantiragin Man United da Paul Pogba yana kan tebur tun watan Yulin da ya gabata. Har yanzu yana yin shawarwari. Bai yanke shawara ba tukunna.

“Man United – babbar kungiya ce. Ba na tunanin cewa wannan kulob din zai ta bukatar rarrashinsa ya zauna a nan.” sako daga Rangnick..[MEN]

#fagenwasanni

 

A kwanakin baya ne aka koma tattaunawa tsakanin PSG – Paris Saint-Germain da wakilan Kylian Mbappé kan sabon kwantaragi, Amma sun tashi ba tare da wani ci gaba ba. dan wasan na Faransa ka’iya fara tattaunawa da Real Madrid kafin a kammala wasanninsu biyu na kofin Zakarun Turai..

(Source: L’Équipe)

#fagenwasanni

 

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *