Wasu ‘yan bindiga da ba a tantance ba a safiyar ranar Litinin sun kai hari a hedikwatar ‘yan sandan jihar Abia da ke Umuahia babban birnin jihar, inda suka kashe akalla mutum guda, kamar yadda kafar talabijin ta Igbere ta ruwaito.
A cewar rahoton, wanda aka kashe din, wani Sufeto ne na ‘yan sanda da ke aikin gadi a gaban ofishin.
An ce ‘yan bindigar da ba a san ko su wanene ba sun kai harin ne da misalin karfe 1 na safiyar ranar Litinin, amma daga bisani jami’an ‘yan sandan da ke bakin aiki suka fatattake su.
An ce ba su yi nasara ba sun yi yunkurin mamaye tashar.
Da aka tuntubi PPRO na rundunar ‘yan sandan jihar Abia, SP Geoffrey Ogbonna, ya ce har yanzu ba a yi masa bayani ba game da lamarin.