Sabanin yadda kungiyoyin kwallon kafa a jihar kano ke zama “daga kwauri sai gwiywa”, wato irin abin nan da ake cewa naka sai naka ko kuma ace kaina nasani, tare da sanya ido da jiran tallafi daga gwamnati wajen cigaba da harkokin wasan, tallafin da kungiyoyin da suka amfana kan rike ba tare da duban na kasa ba,
A karon farko a tarihin karamar hukumar gwale wasu ma sunce a tarihin jihar kano, kungiyar clever warriors kar kashin jagoranci Dr Najib Kurawa ta bada tallafin kayan wasa ga wasu daga cikin kananan kungiyoyi 27 dake yankin karamar hukumar gwale wadanda ke bugawa a matakai daban daban a jihar,
A tattaunawarsa da wakilinmu yayi bada kayan shugaban kungiyar Clever Warriors Dr Najib yace wannan somin tabi ne, mutakar dama zata samu to akwai yiwuwar cigaba da bawa kungiyoyin irin wannan tallafi lokaci zuwa lokaci,
Dr Najib wanda dillalin yan wasane na hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa Agent ya kara da cewa kungiyarsa ta Clever Warriors na kokarin sauya fasalin muamalla tsakanin kungiyoyi dake karamar hukumar gwale laakari da yadda karamar hukumar keda yawan matasa masu wasan kwallon kafa da shygabanni kungiyoyi dake da kishin bunkasa harkar,
Najib yace ” ya zamemin wajibi na taimakawa yan uwana masu kulab da ciwon mai kulab na mai kulab ne”
Kuma zamuyi kokari mu hada kai dan ganin mun bunkasa wasan a tsakanin matasa dake yankika
Kungiyoyin da zasu amfana da tallafin sun hadar da
*Tofa premier*
Dorayi united
Dorayi warriors
Good boys
*Ahlan league one*
Rising stars
Jakore
Chiranci united
New stars
Gwale united
New mandawari
D/babba United
Kabuga United
Raula FC
Countinue mandawari
Sudawa United
Ayaga action
Salanta united
Golden stars dorayi
Ittahat mandawari
Ja’en United
*Division two*
Alma babies
Mujan warriors
D/babba warriors
U/wambai united
Defotibo dorayi
Jakada city
Jakada united
Super boy s/mainagge
A jawabinsu daban daban shugabannin kungiyoyin, Salanta , Kc ,Itihad , Dorayi,Rising, Continue, Sudawa da Gwale United yaba shugaban Clever Warriors sukayi a madadin sauran kungiyoyin inda sukayi alkawarin cigaba da bada gudunmawa dan cimma nasarar da ake bukata,