Rahotanni daga jihar Katsina a arewacin Najeriya na cewa ƴan bindiga sun
kashe wani kwamshina a jihar Katsina a arewacin Najeriya.
Kwamishinan ƴan sanda na jihar ya tabbatar da lamarin a wani taron manema
labarai a ranar Alhamis. Wasu rahotanni sun ce lamarin ya faru ne ranar Laraba
da daddare.
Kwamishinan ƴan sanda ya ce tuni an fara bincike kan mutuwar kwamishinan
kmiyya da fasaha na jihar Katsinan, “don haka babu wani dogon bayani da zan
iya yi yanzu, sai dai a saurara sai binciken ya yi nisa,” in ji shi.
Ya ce tuni aka kai gawar mamacin asibiti.
Bayanai sun ce an kashe Kwamishina Dr Rabe Nasir ne a gidansa da ke rukunin
gidaje na Fatima Shema Estate a cikin birnin Katsina.