Da yammacin ranar (Alhamis) ne ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Fc suka isa Abuja domin halartar gasar gayyatar shugaban kasa da kungiyoyi hudu da za a fara yau a filin wasa na MKO Abiola Abuja. Fagenwasanni.com ta rahoto.
Sauran kungiyoyin da aka gayyata sun hada da Akwa United, Lobi stars da kungiyar Sunshine stars.
A cewar mai magana da yawun kungiyar ta Kano Pillars Fc Rilwanu Idris Malikawa Garu yace kungiyar ta yi tattaki ne da ‘yan wasa ashirin da masu horarwa da kuma wasu ma’aikata.
Malikawa ya ce an gayyaci kungiyoyin hudu ne ta ofishin mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin wasanni Mista Daniel Amokachi.
Ya ce sai masu gida za su yi amfani da gasar wajen inganta matakin shirye-shiryensu na kakar 2021/2022 na Npfl mai zuwa wanda za a fara mako mai zuwa.
Mun yi matukar farin ciki da wannan gasa domin zai taimaka mana wajen sake fasalin kungiyarmu da sanin wuraren da muke da rauni kafin a fara gasar NPFL.
Duk ‘yan wasa ashirin da ke nan tare da mu a Abuja suna cikin koshin lafiya da kuzari
don buga gasar da kuma shirye-shiryen farawa na kakar kwallon kafa ta 2021/2022, Malikawa, ya fada.
A ranar Lahadi ne ake sa ran kammala gasar kuma dukkan kungiyoyin da aka gayyata za su fafata da juna domin samun wanda ya yi nasara.
Kuma Sai Masu Gida za su buga wasan mako na daya a gasar Npfl ta 2021/2022 zuwa Akwa United Fc a ranar 17 ga watan nan a filin wasa na Champions Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.