Ya yi magana ne a Abuja a jiya Litinin a taron shekara-shekara na Hafsan Hafsoshin Soji na shekarar 2021.
Ya kuma jaddada bukatar yin hadin gwiwa a tsakanin jami’an tsaro, musamman a duk ayyukan da sojoji ke gudanarwa.
“Saboda haka, dole ne ku guji duk wani nau’in siyasa wajen gudanar da ayyukanku da kuma taimakon hukumomin farar hula.”
Ya ce, saboda kagara daga hafsoshi da sojoji da kuma sojojin musamman na Najeriya, sannu a hankali ana samun zaman lafiya a duk yankunan da ake fama da rikici a kasar.
Magashi ya roki sojoji da su ci gaba da murkushe ‘yan fashi da ‘yan ta’adda da masu tayar da kayar baya.
Ya ce ana Murkushe ayyukan Boko Haram da ISWAP zuwa mafi kankanta.
Anashi jawabin Babban hafsan sojin kasa, Laftanar-Janar. Faruk Yahaya, ya ce sojoji a shirye suke su kare dimokradiyyar Najeriya da kuma iyakokin kasar.