Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Rundunar Yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar kubutar da wani Yaro dan shekara 17 wanda yan bindiga suka yi Garkuwa dashi a Jihar.

Kakakin rundunar Yan sanda Jihar ASP Muhammed Jalige, shine ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Kaduna.

A cewarsa, Jami’an su wanda suke aikin sunturi ne suka jiyo karar harbe-harbe a Dajin Sabon Birni, inda suka kai dauki domin ganin abinda yake faruwa.

Haka kuma ya ce bayan sun shiga Dajin ne suka yi nasarar korar yan bindigar da suka sace Yaron dan shekara 17, tare da kubutar da shi.

Kazalika, ya ce yan sandan sun dauki Matashin zuwa Asibitin Lafiya a Matakin Farko na Karamar Hukumar Kutungare domin samun kulawar Likitoci.

Kazalika, ya kara da cewa yan bindigar sun sace yaron ne a lokacin da yake aiki a gonar Shinkafa dake Kaduna.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *