Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa SWAN reshen jihar kano Zaharaddeen Sale yace daga yadda aka fara gasar wasan kwallon kafa karo na 10 ts tsakanin kafafen yada labarai a ranar jumaar data gaba abin sai son barka,

A tattaunawarsa da express radio online Shugaban yace laakari da yadda kafafen yada labarun ke dokin fara gasar da yadda alumma suka karbi gasar musamnan a ranar da aka bude ta to ” A gadkiya abin alfarine,abubuwan da muka gani”

Zaharaddeen wanda ya fito daga Radio Nigeria Pyramid yace wasan farko da aka buga da mai rike da kofin ARTV da Pyramid Radio ya kayatar kwarai kuma wasan ya burge kowa,

Dan gane. da yadda akaci gaba da gasar kawo iyanzu Zaharaddeen Sale cewa yayi babu wani korafi ko koke da wata kungiya tayi,kuma hakan bai rasa nasaba da kyakykyawan tsarin da kwamitin shirya gasar karkashin Abubakar Shehu Kwaru yayi,

Shugaban kungiyar marbuta labarin wasan ya kara da cewa ” Ya zama dole na yabawa yan kwamitin shirya gasar LOC musamman kuma shygaban kwamitin saboda juriyarsa da kokarinsa na yin aiki da kowane dan kwamiti Kwaru ya chanchanci yabo ” inji Zaharaddeen

Dan gane da yadda ake kallon gasar nan da wasu shekaru Sale cewa yayi kullum gasar kara karbuwa take kuma ana kokarin sauya mata salo da kawatata muna saran nan gaba gasar zatafi haka

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *