Ba kowanne mutum ne keda daraja da wadansu nasarori tare baiwa ba kamar Khalifan Tijjaniya na Najeriya Muhammadu Sunusi Lamido Sunusi na biyu.
A tautaunawar wakilinmu da Alhaji Laminu Niger yace ” Na zauna na nutsu nayi tunani gami da nazari akan rayuwar Khalifah Sunusi Lamido Sunusi, na tabbatar da cewa a zamanin yanzu da muke ciki zaiyi wahala a samu wani mutum dake da daraja da tarin abubuwa na musamman kamar sa.
Babu abinda Allah bai baiwa Sarki kuma Khalifah Sunusi Lamido Sunusi ba.
Inkafishi kudi baka da Iliminsa, babu wani shugaba a yanzu a kaf fadin Afirka da yakaishi tarin abubuwa na musamman saboda Allah yabashi dukkan wani girma da martaba a rayuwa, saidai muyi masa addu’a Allah yasanya shi a Aljanna firdausi tare da dukkan musulmin dake da zuciya mai kyau irin tasa ta kwarai ameen.
Yana taimakon marasa karfi, shi jigon talakawa ne, yana baiwa dukkan talakawasan taimako da giramasu, idan Khalifah Sunusi Lamido yana tafiya ka tsugana kana gaisheshi yakan saurareka cikin girmamawa da farin ciki sannan yanuna godiyar gareka.
Alh Laminu Niger yakara da cewa “Duk Ilimin da akeso mutum ya samu a rayuwarsa na Boko dana Addini duk yana dasu, haka zalika arziki da iya zaman takewa da hakuri duk yana dasu.
Mawuyacine a zamanin yanzu a samu wani mutum mai kaifin tunani da nazari da dukkan abubuwan dana lissafa yana dasu kamarsa.
Daga karshe Alhaji Laminu Niger ya roki Allah yakarawa Sarki Khalifah Tijjaniya na Najeriya Muhammadu Sunusi Lamidu Sunusi na II Lafiya da zaman lafiya hakuri da daraja, Allah yakara masara daraja da nasarori a dukkan al’amuransa na Rayuwa ameen.