Darakta janar ta gidan talabijin ta ARTV Kano Hajiya Sa’a Ibrahim tace kungiyar kwallon kafa ta ARTV dake matsayin mai rike da kofi ta shirya dan kare kofin a gasar wasan bana tsakanin kafafen yada labarai,
A wata tattaunawa ta musamman da express radio Sa’a Ibrahim cewa tayi babushakka alamu sun nuna ARTV zata iya kare kofin laakari da yadda kungiyar bata huta ba wajen daukar horo tun bayan Nasarar data samu,
Da take amsa tambaya kan damar da kungiyarta ke dashi na kare kofin Babbar Daraktan cewa tayi ” Mu da gaske muke komai kuma tun ba yanzu ba muka shiryawa wannan harkar, shiyasa muka gina filin wasa a harabar maaikatarmu,inda kullum maaikatanmu ke daukar horo saboda mahimmancin wasan a wajenmu”
Dangane da yadda Hajiya Sa’a ke bibiyar kungiyar ARTV. a koda yaushe in suna taka leda babbar daraktar cewa tayi ” Bani da wani abu daya wuce wadannan yaran shiyasa koda yaushe nake tare dasu a wajen daukar horo,wasanni da sauran dukkuan a’lamarin daya shafesu a wajen aiki da koina” ya’ ya nane wasu jikoki ,inji Hajiya Sa’a.
Ta kara da cewa “Jegus Ina tabbatar maka zamu kare kofinmu ” da yarda Allah.