Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa akalla masu dauke da cutar HIV dubu 35 ne suke karbar magani a fadin jihar.

Kwmaishinan lafiya na jihar Dr. Aminu Tsanyawa ne ya bayyana hakan, a lokacin dayake zantawa da manema labarai a yau Laraba, a wurin bikin ranar masu dauke da wannan cutar na duniya.

A cewar kwamishinan, gwamnatin jihar a kowanne lokaci tana kokarin bawa masu wannan cutar gudummawa.

Ya kara da cewa, ana basu kulawa domin gane adadin masu dauke da wannan cutar, domin samo bakin zaren yanda za’a magance matsalar a fadin jihar.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar yanzu haka, ta kirkiri sabbin cibiyoyi 60 a fadin jihar domin dakile yaduwar cutar daga uwa zuwa Da.

Wannnan na zuwa ne jim kadan bayan uwargidan gwamnan Jihar Kano, Hafsat Ganduje ta kaddamar da cibiyar wayar da kan al’umma a satin daya gabata.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *