Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) a jihar Katsina ta ce ta cafke wata mota makare da kudi sama da Naira miliyan 71 da ake zargin na harkallar miyagun kwayoyi ne, Daily Nigerian ta ruwaito. Mukaddashin Konturola na rundunar, Dalhat Wada-Chedi, ya shaida wa manema labarai a Katsina ranar Litinin cewa an kama kudaden ne a farkon watan Nuwamba.
Hukumar kwastan ta Najeriya ta tsananta bincike dan hana miyagu safarar kayan da aka haramta shigowa dasu cikin kasa tare da dakile safarar makamai da aka addabi kasarnan dasu,