Tsohon Ministan Sufurin Jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya ƙaryata rahoton da a ke cewa Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa, EFCC ta kama shi a jiya Talata.
Rahotanni sun bayyana cewa EFCC ta kama tare da titsiye Fani-Kayode tsawon awanni.
Da ya ke maida martani, Fani-Kayode, wanda a ke wa laƙabi da FFK, ya wallafa a shafinsa na instagram cewa rahotannin da a ke yaɗawa cewa EFCC ta kama shi ba haka bane.
Ya ce gayyatar shi Hukumar ta yi kuma bayan ya basu bayanai sai ta yi amfani da matsayinsa a ƙasa ta sallame shi.
Haka zalika rahotanni sun sake bayyana cewa EFCC ta titsiye Fani-Kayode ne a kan zargin takardun bayanan lafiya na ƙarya.