Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gabanin fara gasar wasan kwallon kafa tsakanin kafafen yada labarai dake jihar kano da kungiyar marubuta labarin wasanni ta kasa shiyyar reshen jihar kano suka shirya,

Daya daga cikin jagororin yan wasa Amiru Inuwa Kachako yace kawo iyanzu da gidan radiyon express radiyo shiri ya kankama duba da yadda hukumar gudanarwar gidan radiyon ta bada kulawa ga yan wasa na samar da kayayyakin wasan a lokacin da ake bukata,

Amiru Inuwa wanda dayane daga cikin fitattun yan wasa a kungiyar data kare a matsayi na biyu a gasar data gabata ya kara da cewa kawo iyanzu sun koyi darasi, kuma a wanna lokacin yan wasa sun shirya dan tun karar kalubalen dake gabansu,

Da yake amsa tambaya kan matsayin kungiyar a wasan daya gabata tsakanin kafafen yada labarai Amiru cewa yayi “Wannan lokacin da izinin Allah zamuyi kokari fiye da wancan lokacin laakari da yadda yan wasan da masu horarwa karkashin Salisu Musa Jegus da Muhammad Auwal Tudun Murtala ke gudanar da aikinsu ba gajiyawa da hadin kai da kaunar juna, wanda hakan wata almace da ke alamta irin nasarar da akesa ran samu

Dan wasan ya kara da cewa. yadda rukunin da suke ciki ya nuna akwai kalubale a cikinsa duba manya kafafen yada labaru dake ciki da suka hadarda irinsu Maaikatar yada labarai, freedom Radio, BUK Radio da Wakilan kafafen yada labarai na kasa Correspondent Chapel wadanda mayan kingiyoyine kuma suna da yan wasa,amma muma ba kanwar lasa bane ” Mun shirya ” inji Amiru Inuwa Kachako

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *