Shugaban karamar hukumar birnin kano da krwaye Hon Faizu Alfindi yayi alkawarin gyara rumfunan da gobara ta kone a shahararriyar kasuwar Kurmi a ranar Litinin da ta gabata.
Kwamared Alfindiki wanda ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar jajantawa kasuwar da abin ya shafa da ke tsakiyar birnin Kano, inda ya bayar da tallafin naira miliyan biyu ga ‘yan kasuwar da abin ya shafa.
Alfindiki ya bayyana cewa sun bayar da tallafin ne domin rage radadi ga wadanda abin ya shafa domin sake fara sana’arsu ta yau da kullum.
Shugaban ya bayyana faruwar gobarar a matsayin bala’i da ta lakume zunzurutun kudi na miliyoyin naira musamman a wuraren shagunan sayar da littattafai na kasuwar.
Daganan sai Kwamared Alfindiki ya godewa Kwamishinan Kananan Hukumomi, Alhaji Murtala Sule Garo bisa yadda suka yi wa Majalisar Dokoki ta Garin farfado da harkokin tattalin arziki a kasuwar.
Inda ya roki Allah Madaukakin Sarki da ya kiyaye afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.
A nasa jawabin shugaban kungiyar kasuwar Kurmi, Alhaji Ya’u Karas ya yaba da wannan karimcin da shugaban karamar hukumar Faizu Alfindiki yayi, inda ya kara da cewa hakan zai basu damar dawowa sanaar su cikin hanzari
Don haka Karas ya bukaci mambobin kungiyar da su yi amfani da wannan gudummawar don fara kasuwancin su.