Shugaban Kamfanin Tashar Tsandauri ta Dala Inland Dry Port Alhaji Ahmed Rabiu yace bunkasa harkokin wasanni hanyace mafi sauki wajen bunkasar tattalin arziki da cigaba alumma,
A wata tattaunawa ta musamman da Express Radio Alhaji Ahmed Rabiu yace, ya dade yana mamakin yadda yake jin ana cewa ansayi Dan wasa ka kudi Fam miliyan Casa’in (90) ko Dala miliyan Dari da Ashirin ($120m) abin da yace ya sashi yin tambaya cewa ” Dalar da ake kashewa ce ko wata Dallar ce ? ” inda yace saina tabbatar cewa Dollar da ake maga itace dai,
Da yake amsa tambaya kan yadda harkokin wasa zasu taka rawa wajen bunkasa tattalin arziki tsohon kwamishinan ciniki na jihar kano cewa yayi. Kasashen da sukaci gaba a duniya na samun makudan kudin shiga da harkokin wasanni, inda saboda cigaban ya sanya manyan kamfanoni kwace harkokin tare da zuba jari cikin kungiyoyi da gina manya manyan filayen wasanni da suke kawowa masanaantun kudin shiga,inda yace ” zakaga an dika dan zanen ko hoton kamfani a filin wasa wanda hakan kan tallata kamfanin baa kasarsa kawai ba har a duniya baki daya,
Kan yadda wasanni ke da tasiri manajan daraktan na Dala Inland port cewa “Mafi yawan alumma ayau suna shaawar kallon wasanni kuma sanya sunan kamfani a filin wasa na dauka hankalin jamaar da suke kallon wanda hakan wani tadirine na tallata haja” inda yace mutane da rayuwa ta bawa damar motsawa dasu “Active population” kamar yadda ya fadi a harshe turanci ne ke samun damar da ake damawa dasu kuma wasanni ne suka bada wannan dama,
Daya karin haske kan tasiri wasanni ga rayuwar Dan Adam cewa yayi akwai bambanci Mai fadin gaske tsakanin wanda yake motsa jiki da ci ka kwanta wajen samun lafiyar jiki inda yace ” Kai ko kallon wasa kake lafiyarka tafi ta wanda baya kallon wasa saboda kai kana kallon wani abu da yake motsa zuciyarka sabanin wanda baya samun abinda yake motsa tasa” inji Ahmed Rabiu.
Da yake amsa tambaya kan tasirin kulla dangantaka tsakanin kamfanin Dala Inland Dry Port da kungiyar marubuta labarin wasanni manajan Daraktan Kamfanin cewa yayi ” kulla alakar babbar nasarace ga kamfanin mu saboda tasirin da kungiyar da yayan kungiyar ke dashi wajen aikinsu da yadda suka rike sanaarsu da gaskiya da kwazo ”
Inda ya kara da cewa ta hanyar marubuta labarin wasanni labarun da tallace tallacen zasu isa cikin sauki da sauri, kuma ance mai kamar zuwa kan aika,
Dan gane da yadda zaa samar da cibiyoyin wasanni manajan Daraktan cewa yayi lallai akwai bukatar kamfanoni da manya masu kudi su shigo cikin harkokin wasanni kamar yadda kasashen da sukaci gaba suke inda yace ” Duk duniya kamfanoni ne da attajirai ke ginawa da samar da kungiyoyi na wasanni ba gwamnatoci ba, saboda haka ya zama wajibi ga masu hannu da shuni su shigo hsrkokin wasanni da samar da kyakykyawar makoma ga matasan dake da Basira dan kau dasu daga mummunan tunani,
Karshen kashin farko na hirar kenan a taremu a kashi na biyu