Dillalin yan wasa kuma shugaban Kungiyar kwallon kafa ta Clever Warriou Dr Najib Kurawa ya bayyana dillancin yan wasa da cewa harkace dake bukatar hakuri, Hangen nesa da zurfin Tunani,
A tattaunawarsa da manema labatai a wani shirina musamman Najib Kurawa yace matakan da ake bi wajen samu da rainon dan wasan da zai iya gogayya a babban mataki na bukatar hakuri,
Da yake karin haske kan yadda dan wasa ya kamata ya zama dan gogayya da manya yan wasa Dillalin yan wasan cewa yayi, kwallon kafa a fili take kuma abubuwan da ake bukata ga Dan wasa shima a fili yake saboda haka abubuwan da Dan wasan ke bukata shine Iyawa da wayewa da wasan da yanayin da ake wasan a cikinsa,
Kan yadda yake batun Iyawa Dr Najib cewa yayi” Ba kowane Dan wasane ya iya wasan ba,” E nace ba kowane ya iya wasan kwallon kafa ba, dan cikin yan wasa 10 a kyar zaka sami 4 da suka fahimci yadda wasan yake, kamar yadda ake bukata a Turai, ” mun taba kai yan wasa sunyi kwallo amma juriyarsu bata kai ba dole saida suka dawo dan neman ” Fitness”
Kan kalubalen da dilalan wasa ke fuskanta Dr Najib Kurawa cewa yayi ” Agent na bogi sune kalubale kuma su sukafi baki saboda karyarsu ” fatanmu Allah yasa shugabanni kungiyoyi su gane,
Da yake amsa tambaya kan kungiyar da yake wakilita Dr Najib cewa yayi kungiyata ta clever daban kuma dillancina na yan wasa daban, shi aiki dillanci na kowane ba sai lallai Dan clever warroius ba,