Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

 

An yi garkuwa da wasu matafiya da ba a tantance adadinsu ba a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Wani faifan bidiyo da aka fitar ta yanar gizo ya nuna wasu motoci guda biyu babu kowa, wadanda da alamu an bar su a tsakiyar babbar hanyar.

Wani shaidan gani da ido da ke tafiya a kan hanyar ya fitar da wani dan takaitaccen faifan bidiyo da ke nuna wasu motoci guda biyu da aka yi watsi da su a yayin da ya ke bayyana cewa an sace mutanen.

A cikin faifan bidiyo na dakika 31, an ji wanda ke bayan kyamarar yana ihu yana cewa, “Ya Allah, sun dauki abokanmu, daga Kaduna muke tahowa. Yau 21 ga Nuwamba, shekarar 2021, ya Ubangiji, Ubangiji mai aminci ne, na gode da ceton rayukanmu.”

Har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta mayar da martani kan faifan bidiyon ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige, bai amsa kiran da aka yi masa ba don tare da tattaunawa kan faifan bidiyon. Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *