Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

A Najeriya, daruruwan tsoffin ‘yan kungiyar Boko Haram da suka tuba suka gabatar da kansu ga Dakarun kasar, suka yi zanga-zanga a sansanin da aka ajiye su da ke kusa da Maiduguri, jihar Borno.

Tsoffin mayakan kungiyar ta Boko Haram na bukatar a basu damar yanka shanu don samun nama da za su ci.

Sun yi boren ne dauke da makamai da suka hada da adduna, gatari da sanduna suna barazanar kashe duk wanda ya fice daga sansanin da aka jibge su a lokacin boren.

Wannan na nuna irin gagarumin aikin da Hukumomin kasar ke yi don sauya ra’ayoyin tsoffin mayakan kungiyar ta Boko Haram don su iya zama cikin al’umma bayan da aka kwashe shekaru 12 ana fafata yaki da su.

Kimanin tsoffin mayakan kungiyar Boko Haram 250 da suka hada da maza da mata da kananan yara, wadanda aka tsugunar a unguwar Gidan Taki dake bayan garin Maiduguri suka shiga boren.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *