Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban karamar hukumar Gwale Khalid Ishaq Diso yace laakari da gudum mawar da wasu daga cikin matasa ke bawa karamar hukumar da shi kansa ya sanyashi sake kusanto dasu cikin gwamnati musamman wajen harkar wayar da kai da yada sahihan labaru da matasan keyi a kafafen sadarwa,

Dayake jawabi yayi basu takardun kama aiki a matsayin mataimaka na musamman a sakatariyar karamar hukumar Jagoran Gwale Sabuwa Khalid Ishaq Diso ceqa yayi ” Allah ne ya baku wannan dama duba da irin rawar da kuke takawa wajen yada labarun ayyukan da karamar hukuma keyi a koda yaushe ”

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa ” kokarin mutum shine yake bashi damar samun abubuwa musamman irin wannan damar” saboda haka kowa ya koma mazabarsa ya cigaba da yada manufofin gwamnati a matakin jiha da karamar hukuma wanda hakkan shine zai bawa mutane damar fahimtar ayyukan gwamnati cikin sauki,

Daganan sai ya ja hankalin wadanda suka rabauta da mukaman da suyi amfani da abubuwan da zasu samu waken rike kansu da tallafawa yan uwansu

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *