Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Dan Majalisar wakilan tarayyar Najeriya, mai wakiltar kananan hukumomin Zuru, Fakai, Danko Wasagu, da Sakaba, da ke jihar kebbi, kuma Shugaban Matasan’yan majalisun Najeriya, kana kwamitin Sharia a zauren Majalisar wakilan Najeriya,

Shugaban Matasan’yan majalisun Najeriya Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya bayyana cewa, gwamnatin Najeriya, tana sane, da irin muhimmiyar rawar da Matasa ke takawa wajen cigaban al’umma, don haka gwamnatin tarayya tasa za ta tabbatar da suna samun horo yadda ya kamata, da bunkasa walwalar su, da samar da ayyukan yi, ga matasan Najeriya,

Da yake jawabi yayin taron da suka gudanar, a birnin Legas, Tukura ya ce wannan matakin ya biyo bayan tuntubar, iyaye da jagororin al’umma, ya kara da cewa matasa za su marawa gwamnatin baya, tare da fatan zai yi nasara la’akari da kwazon su da biyayyar su ga shuwagabannin,

Tukura ya bayyana gamsuwar sa kan tsarin tare da taya gwamnatin Najeriya murnar samun wannan matakin domin tabbatar da jindadi da walwalar matasa,

A lokacin kaddamar da wani shiri na taimakawa matasa wanda ya gudana, a birnin Legas, Tukura, ya ce wannan tsarin zai rika taimakawa, Matasa dubu 20, da suka kammala jami’a a gurabe, daban daban, a kowacce shekara,

Wannan shirin zai taimakawa matasa samun aikin yi na hadin gwiwar gwamnatin Najeriya,

Yayin da yake yabo Honarabul Kabir Ibrahim Tukura, ya jinjinawa gwamnatin Najeriya ya kuma jaddada cewa gwamnatin Najeriya zata cigaba da daukar duk wani matakin kyautatuwa da walwalar matasa da cigaban su dama karfafa musu gwiwa a fadin Najeriya

 

Daga Abbakar Aleeyu Anache,

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *