Amon ya bayyana haka ne a ranar Talata yayin zaman kare kasafin kudin 2022, a gaban kwamitin rundunar sojin sama na majalisar dattawa.
Ya ce an lalata ‘yan ta’addan tare da kassarasu tare da yi musu asarar mayaka da makamai, wanda ya sa da yawa daga cikinsu suka mika wuya da radin kansu. “Hakan da ake bukata cikin dabara tuni aka tsara taswira don murkushe ragowar ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a kauyuka da sansanonin sojoji da nuna cewa har yanzu suna da karfi.
“A bisa babban aikin rundunar sojin sama da sauran sojoji gaba daya, ana kare martabar yankin Najeriya daga ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga, wadanda nan da wani lokaci, za a kawar da su gaba daya,” in ji shi.
Ya ce kamar yadda aka yi amfani da kasafin kudin shekarar 2021 ga rundunar sojin sama ta hanyar da ta dace wajen hukunta masu tada kayar baya da ‘yan ta’adda da kuma kyautata jin dadin jami’ai, haka nan za a yi amfani da kason na shekarar 2022 ta hanyar da ta dace. “A yayin da ake fuskantar kalubalen da ake fuskanta, taka tsan-tsan da rikon amana sun kasance jagorar aiwatar da kason kasafin kudin da rundunar sojojin saman Najeriya ta yi,” in ji shi.
Kafin zaman majalisar ya shiga rufe kofa, shugaban kwamitin Sanata Bala Ibn Na’Allah (APC, Kebbi) ya umurci sojoji da su yi amfani da duk abin da suke da shi wajen fatattakar ragowar ‘yan tada kayar bayan da kuma karbe dazuzzukan da ‘yan fashi, masu garkuwa da mutane da duk wani nau’in masu laifi ke amfani da shi.
“Rundunar sojin sama da kuma karin sojoji gaba daya sun cancanci yabo daga ‘yan Najeriya dangane da yaki da ‘yan tada kayar baya da ‘yan bindiga amma ‘yan Najeriya na son a fatattaki wadannan makiyan kasa gaba daya da wuri.
“A gare mu a wannan kwamiti da kuma a Majalisar Dokoki ta kasa, muna bukatar a ba da kudade ta fuskar sayan makamai, kayan yaki da inganta jin dadin jami’ai cikin azama a cikin sojoji za a yi shi tun da shi kansa tsarin mulki shi ne tsaro da jin dadin ‘yan kasa,” in ji shi.