Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Kungiyoyin kwadago na cibiyoyin bincike a Najeriya sun bukaci shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya ceto cibiyoyin daga durkushewa, saboda halin tagayyara da cibiyoyin ke ciki.

A taron manema labarai da gamayyar kungiyoyin kwadagon na cibiyoyin bincike ta kira, sun bayyana cewa shekaru da dama gwamnatin tarayya take rikon sakainar kashi saboda rashin bada isasshen kudade don inganta ayyukan bincike a cibiyoyin dake samar da duk wani abinda al’umma ke amfani da shi, tun daga kan magunguna, ma’adinai, karafa, ayyukan gona, muhalli, cimaka da sauransu.

Komared Luka Malaya Maigari yace sau talatin da uku sukayi zaman tattaunawa da gwamantin tarayya amma har yanzu hakarsu bata cimma ruwa ba, don haka suka shiga yajin aiki.

Komared Umar Dan Halilu ya ce sun fito ne su yi wa gwamnatin tarayya tuni kan alkawuran da tayi.

Voa ta ruwaito  shugaban hukumar binciken harkokin noma ta tarayya, Farfesa Garba Hamidu Sharubutu yace gwamnati na daukan matakan warware matsalar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *