Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya mika ta’aziyyarsa tare da jajanta wa shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote bisa rasuwar dan uwansa Sani Dangote, wanda shi ne mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote.
“Mun samu labarin rasuwar wannan mutumi, Alhaji Sani Dangote, cikin kaduwa. Jihar Kano, kasarmu Najeriya da ‘yan kasuwa sun yi hasara kuma hazikin dan” Ganduje ya bayyana haka a wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar ya fitar a ranar Litinin.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Alhaji Sani Dangote ya rasu ne a wani asibiti dake kasar Amurka bayan ya sha fama da jinya a daren Lahadi.
A cewar sanarwar, Gwamna Ganduje ya koka da cewa, mutuwar ba wai kawai ta tayar da hankali ba ce, ga iyalan mamacin “… amma ga dukkan mu musamman ‘yan jihar Kano. Mun yi asarar wani abu mai daraja a cikin ’yan kasuwa.”
“Don haka a madadin gwamnati da nagari na jihar Kano, ni gwamnan jihar Kano, ina mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalan Alhaji Sani Dangote, da dan uwansa, Alhaji Aliko Dangote, bisa rasuwarsa. .”