Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Mukaddashin daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Bernard Onyeuko, shine ya bayyana hakan yau a Abuja, yayin da yake yiwa manema labarai karin haske kan ayyukan da sojojin suka yi tsakanin ranakun 29 ga watan Oktoba zuwa 11 ga watan da muke ciki na Nuwamba.

Onyeuko ya kuma bayyana cewa an kubutar da mutane 42 da aka yi garkuwa da su a wasu ayyuka daban-daban da aka gudanar a shiyyar cikin kwanakin.

A karkashin Operation Safe Haven, Onyeuko ya ce sojojin sun ci gaba da taka-tsan-tsan tare da sintiri na kasa da na sama don hana masu aikata laifuka ‘yancin yin aiki.

Ya ce al’amuran rashin tsaro a jihar Filato sun lafa kadan a cikin wannan lokaci duk da cewa an samu wasu matsaloli a wasu wuraren.

Ya kara da cewa sojoji sun ceto mutane 33 da aka yi garkuwa da su daga hannun ‘yan bindiga tare da kama wasu masu laifi 23 a cikin kwanakin.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *