Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Gwamnatin Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ta yi kira da yan Najeriya cewa, da akwai bukatuwar yin noma ko da a cikin gidaje ne saboda a rage radadi da tsananin rayuwa wanda dama ya samo asali ne saboda hawhawar farashin kayayyakin masarufi.

Ministan kudi, tsimi da kididdiga, Zainab Ahmed a wani jawabi da ta gabatar ranar Laraba a wani shiri na “Siyasa a Yau” na gidan talabijin din “Channels TV’s, a yayin da ta ke tsokaci akan hauhawar kayayyakin masarufi, ta bayyana cewa;“yan Najeriya ba za su fada yanayin yunwa ba. Don haka, muna karfafawa yan Najeriya gwuiwa sa su yi noma koda a kusa-kusa da gidajensu ne”.

A yayin da aka tambayeta, shin ko gwamnatin Buhari ta samar da saukin rayuwa wa talakawa duba da irin tsananin rayuwan da su ke ciki, wanda ya samo asali ne saboda hauhawar farashin kayayyakin masarufi, Mrs Zainab ta ce;”Ina matukar tausayawa yan kasa. Hakika Shugaban kasa yana damuwa da jin zafin halin kuncin da yan kasa su ka tsinci kansu a ciki – Musamman yanda farashin kayayyakin masarufi ya ke ta tashi ba kyaukyautawa”.

Dadin dadawa, ta kara bayanin cewa, tsadan kudin sufuri na daya daga cikin abubuwan da ya ke haddasa hauhawan farashin abinci. Amma duk da haka, Shugaban kasa yana kafa wani tushe domin samun ci gaban kasa.

Ministan ta kara da cewa;“Ya dace mu yi wannan tsarin tun yanzu don idan ba haka ba, halin da za mu tsinci kanmu a shekaru ma su zuwa, sai ya ninka halin tsananin da wahalan da mu ke ciki a yanzu”.

Idan dai baku manta ba, a farkon watan data gabata, Octoba, Shugaban kasa Muhammad Buhari, a zancensa da ya gabatar na murnan samun yancin kai, ya daura alhakin hauhawan farashi akan mutanen da su ke siyan abinci su boye saboda su sa abinci ya yi karanci don hakan shi ne zai ba su daman samun riba.

A wani bincike da gidan jaridarmu ta Manuniya ta yi, a watannin baya, farin waken da ake sayarwa akan farashin dubu talatin, to a yanzu ana sayar da shi ne akan dubu dari a wasu yankunan kasar.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *