Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya yi tsokaci dangane da irin himma da kwazon da yan Najeriya su ke yi a yayin da wasu al’amura ya fita da su kasashen ketare inda ya bayyana cewa, su na kwazon ne saboda ingantaccen ilimin da su ka samu tun farko a cikin Najeriya.

Muhammad Buhari, ya bayyana hakan ne a yayin ganawarsa da Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Daular Larabawa (UAE) Shaikh Shakboot Alnahyan. Ganawar nasu da ya gudana a kasar Faransa ranar Juma’a a gefen taron zaman lafiya da suke halarta.

A wani tsokaci da kakakin fadar Shugaban kasa, Femi Adiseni ya fitar, Shugaban kasa Muhammad Buhari ya suffanta yan Najeriya a matsayin “Masu Gogayya a cikin Najeriya da kuma kasashen ketare” inda ya shawarci yan kasa da su ci gaba da kara kaimi.

A cikin zancensa yana cewa: “Akwai ‘yan Najeriya a ko’ina, masu ƙwazo. Kuma ƙwazon nasu na farawa ne tun daga gida (Najeriya), inda suke samun ingantaccen ilimi, su shiga sana’o’i sannan kuma su wuce ƙasashen waje.”

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *