Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Lauyoyin da su ke ba wa shugaban tsageran IPOB, ma su fafatukar kafa kasar Biyafra, Nnamdi kanu sun nuna damuwa da fushinsu dangane da yanda aka hana su shiga kotu don bayar da kariya wa shugaban IPOB Nnamdi kanu a gaban kuliya.

Lauyoyin, Ifeanyi Ejiofor da Bruce Fein sun bayyana damuwarsu ne a lokacin da su ke zantawa da manema labarai a yau, a babban birnin tarayya Abuya bayan kotu ta dage sauraron karar ta su zuwa sabuwar shekara.

Lauyan, a yayin da ya ke gabatar da jawabi wa yan jaridu, ya bayyana cewa sun yanke tsammanin cewa kotun Najeriya za ta yi ma su adalci don haka, za su dauki karar su kaishi kotun kasa-da-kasa.

A cewar Ifeanyi Ejiofor;”Bana tunanin za mu ci gaba da gudanar da shari’a da wannan kotun na Najeriya. Mu na kyautata zaton za mu janye karar daga wannan kotun. Domin, bisa la’akari da abun da ya faru a yau, sam ba mu da sauran aminci cewar za a yanke hukunci bisa gaskiya a wannan shari’ar

Dayan lauyan, Bruce Fein ya koka tare da fadin;”Yau fa karo ta biyar kenan da ake hana mu shiga cikin kotu don mu bayar da kariya duk da cewar ita kotun ne ta yarda da cewa Nnamdi kanu, idan ya so, zai iya zuwa da mutane guda uku koma su waye ne”

“Don haka, ina sanar da yan Najeriya cewa zan dauki wannan karar na kaishi kotun kasa-da-kasa domin ya bayyana karara cewa, kotun najeriya ta na ha’intarmu ne kawai”.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *