Contact Information

Theodore Lowe, Ap #867-859
Sit Rd, Azusa New York

We Are Available 24/ 7. Call Now.

Malaman Jami’ar dake garin Zuru a jihar kebbi sun koka da rashin albashi na tsawon watanni 10, Jami’ar dai garin Zuru mallakar gwamnatin tarayyar Najeriya ce kuma Malaman Jami’ar, sun shiga wata na 10 ba tareda jin albashi ba.

Gwamnatin Tarayya Najeriya ta kwashe, tsawon watanni 10 batare da ta biya Malaman Makarantar albashinsu ba, wanda hakan yasa Malaman Makarantar shiga wani mawuyacin halin rayuwa.

Ta bakin wani daga cikin malaman da ya buƙaci a sakaya sunan sa ya kira da gwamnatin tarayya da ta duba lamarin da suke ciki na rashin albashi har tsawon wata 10.

Majiyar tamu yaci gaba da cewa “muna cikin mawuyacin hali bisa wannan lamarin ta yarda gwamnati tayi watsi da mu kuma muna bukatar kulawar gwamnati a wannan lamarin”.

A nata ɓangaren itama wata malamar Jami’ar da ta buƙaci a boye sunanta “tace za ta fara sana’a domin ana samun gibi yanzu a albashin Gwamnati tace ta nemi bashi amma har yanzu bata samu ba.

© Zuma Times Hausa.

Malaman Makarantar, sun bayyana cewa rayuwa tayi masu matukar wahala a wannan halin da suke ciki yanzu.

Daga Abbakar Aleeyu Anache.

Share:

administrator

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *